Sokoto ta gano malaman bogi 4,000

Image caption Gwamnan jihar Sokoto, Aliyu Wammako

Gwamnatin jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya ta gano malaman firamare na bogi kusan 4,000 da ke karbar albashinta duk wata.

Shugaban hukumar samar da ilimin bai daya a jihar SUBEB, Alhaji Ibrahim Dingyadi ya ce sun gano malaman bogin ne sakamakon binciken da suka shafe watanni hudu suna yi a makarantun firamaren jihar.

A cewarsa, sun gudanar da binciken daga watan Yuli zuwa Okotoba a makarantun firamare 1,965 da ke jihar.

An dade ana fuskantar matsalar samun malaman bogi a Najeriya, inda a galibin jihohin kasar idan har aka gudanar da bincike za a gano dubban malaman da sunayensu ke kan takarda amma a zahiri ba sa nan.

Karin bayani