An kai harin kunar bakin wake a Tunisia

Tunisia
Image caption Tunisia

An kai harin kunar bakin wake a gaban wani otal da ke garin Sousse a gabar tekun Mediterranean a kasar Tunisia.

Wani ma'aikacin otal din ya shaidawa da BBC cewa da misalin karfe 8:45 GMT aka kai harin amma maharin ne kawai ya halaka.

Haka kuma, jami'an tsaro sun kama wani da suke zargin dan kunar bakin wake ne a kabarin tsohon shugaban kasa Habib Bourguiba.

Mr Bourguiba shi ya mulki Tunisia bayan samun 'yanci daga France; an yi masa juyin mulki a 1987 kuma ya rasu shekaru 13 da suka wuce.

Kabarin na sa na garin Monastir ne mai nisan kilomita 20 daga Sousse.

Tun bayan juyin juya halin 2011 wanda ya hambarar da gwamnatin shugaba Zine al-Abidine Ben Ali, ake samun karuwar hare-hare a Tunisia.