'Yan sanda a Kano sun tursasawa malamai

Image caption 'Yan sanda sun hana malaman jami'ar gudanar da gangami

An yi takkaddama tsakanin 'yan kungiyar malaman jami'o'i ta Nigeria watau ASUU, reshen Jami'ar Bayero a Kano da kuma 'yan sanda, wadanda suka hana 'yan kungiyar fita daga harabar jami'ar a yayin da suke yin wata zanga- zanga.

Kungiyar malaman jami'o'i ta Nigeria ASUU reshen jami'ar Bayero ta kira zanga-zangar ce a ranar Alhamis domin kara jaddada matsayinta a kan yajin aikin da take yi.

Kungiyar ta ce duk da cewa gwamnatin kasar ta hana malaman da suke yajin aikin albashi, hakan da ma duk wani mataki ba zai sa su ja da baya a fafutukar da suke yi ba, har sai sun cimma manufarsu.

A wata sabuwa kuma wasu kungiyoyin rajin kare hakkin masu karbar fansho suka gudanar da wata zanga-zanga a kofar harabar hukumar kare hakkin bil adama ta Nigeri, inda suka gabatar da kokensu kan abin da suka ce nuna halin-ko-in-kula da hukumomin kasar ke yi game da halin da wadanda suka yi murabus daga aiki ke fuskanta.

Kungiyoyin dai sun bukaci hukumar kare hakkin biladama da ta bi kadin hakkokin wadannan mutane don kawo karshen matsalolin da ke addabarsu.

Karin bayani