An tsare 'yan China da India su 46 a Ghana

Image caption Inda ake hako zinare a Ghana

'Yan sanda a Ghana sun tsare 'yan kasashen China da India su 46 bisa zargin hako zinari ba bisa ka'ida ba.

An damke mutanen ne a wani samame a cikin dare a lardin tsakiyar kasar inda suka ayyukansu a kusada rafin Offin.

A bana Ghana ta tasa keyar 'yan kasar China fiye da 4,500 saboda saba ka'idar hako zinare a cikin kasarta.

Dokar kasar Ghana ta haramtawa 'yan kasashen waje ayyuka a kananan wuraren hako zinare.

'Yan sanda sun ce 'yan China 43 da 'yan India 3 da aka tsare, za a duba takardunsu, kuma idan basu da cikakkun takardu za a tilasta musu komawa kasashensu na asali.

Karin bayani