An jinkirta shari'ar shugaba Kenyatta

Kotun tuhumar manyan laifuka ta duniya ta dage shari'ar Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta har ya zuwa cikin watan Fabrairun badi.

Lauyoyin Mr Kenyatta a makon da ya wuce sun bukaci da a jinkirta soma shari'ar, suna cewar ana bukatar shi a gida domin ya tinkari sakamakon harin da aka kai a rukunin kantunan nan na Westgate a Nairobi.

An dai tuhumi Mr Kenyatta da laifin cin zarafin bil adaman da aka aikata a lokacin tashin hankalin bayan zaben shekara ta 2007.