Zanga-zangar hukuncin fyade a Kenya

fyade a kenya
Image caption Yarinyar da aka yiwa fyade

Ana jerin gwano a Nairobi, babban birnin Kenya domin isar da takardar koke ga 'yan sanda game da sassaucin hukuncin da aka yiwa mutanen da ake zargi da yiwa wata yarinya fyade.

Fiye da mutane miliyan daya da rabi ne su ka rattaba hannu kan takardar koken ta intanet, wacce ke neman 'yan sanda da su bi wa yarinyar hakkinta.

Ana dai zargin mazajen shida ne da yi wa 'yar shekara 16 fyade tare da jefa ta cikin shadda bayan ta fita daga hayyacinta.

Sai dai bayan 'yan sanda sun kama uku daga cikinsu sai suka yanke musu hukuncin yanke ciyawar da ke bakin caji ofis din su kawai.