Mata masu dako daga Morocco zuwa Spain

Alfadarai mata na Melilla
Image caption Alfadarai mata na Melilla

Garin Melilla wani yanki ne na kasar Spain da ke makwabtaka da Morocco. A kullu yaumin tun da duku-duku kura kan turnuke kan iyakar kasashen biyu. Kujuba-kujubar 'yan kasuwa da ke kokarin tsallaka iyaka da hajarsu ce ke tada kurar.

Kayan sun hada da gwanjo, yadudduka, da kuma kayan shafe-shafe wadanda za'a sayar a kasuwannin Morocco.

Dubunnan mutane ne ke cincirindo a wurin mai cike da hayaniya.

Ko ina ka duba manya manyan dilolin kaya ne a cikin kwalaye da buhunhuna da aka daure da igiya. A durkushe a karkashin kayan nan kuma matan Morocco ne da ke daukar wadannan tarin kaya. Mutanen yankin na kiransu alfadaran mata na Melilla.

Matukar 'yar dakon za ta iya daukar kayan a bayanta, doka ta amince ta wuce da su a matsayin kayan amfani don haka babu harajin da za ta biya. Wannan ya sa 'yan kasuwa da dama ke baiwa matan kayansu su yi musu fito ta hanyar dako.

Latifa na daya daga cikin daruruwan matan da ke wannan sana'a ta daukar dakon kayan gwanjo da nauyinsu ya wuce 60kg wate fiye da buhun siminti guda. Shekarunta 24 ta na wannan aiki kuma kudin dakonta ya kama ne daidai da Naira 700. Sai dai ba'a son ranta ta ke aikin ba.

Ta ce; "Ina da iyalin da na ke ciyarwa. 'Ya'yana hudu kuma babu mijin da zai tallafi min - tun da muka rabu saboda duka na da yake yi."

Yawancin matan da ake kira alfadaran Mellila zawarawa ne kamar Latifa da ke da nauyin 'ya'ya a wuyansu.

Image caption Mata ne suka dauko wadannan kayayyakin a bayansu

Rayuwa ta na da tsanani a wannan bangare na Morocco kuma wannan shi ne kadai aikin da za su iya samu. Wasu daga cikinsu kan dauki dakon sau uku zuwa hudu a kullum dauke da kayan da nauyinsu ya zarta 80kg.

Kudin da ake biya ya kan bambanta kuma matan na kukan cewa 'yan sandan Morocco su na karbar cin hanci kafin barinsu su wuce.

Cece-kuce

Ana cigaba da cece-kuce a Melilla dangane da wannan batu. Emilio Guerra na jam'iyarr Union Progreso y Democracia ya ce "Wadannan mata na jefa rayuwarsu cikin hatsari - tun da an sha samun masu mutuwa saboda wannan dako. Don haka ya kamata a fito da matakan da za su kyautata yadda su ke wannan sana'a."

Image caption Wasu daga cikin matan sun tsufa

Sai dai mai baiwa gwamnatin Melilla shawara kan tattalin arziki Jose Maria Lopez bai amince ba. Ya ce; "Ana samun alheri sosai a wannan harka. Wadansu daga cikin 'yan dakon nan ba su da wata hanyar samu sai wannan. Da gaske ta na da matukar wuya amma abinda suke samu yafi abinda mafi yawan ma'aikatan Morocco ke samu."

Can a kan iyakar Bario Chino kuwa, alfadarai matan ne kokawa da yadda su ka ce maza na neman karbe musu sana'a saboda rashin aikin yi da ake fama da shi a Morocco. Sai dai kuma duk da wannan tsayin daka da su ke kan wannan aikin karfi, matan sun ce burinsu shi ne a samu cigaba a kasar ta yadda 'ya'yansu ba zasu gaje su ba.