Syria ta gama lalata makamai masu guba

Lalata makaman Syria
Image caption Lalata makaman Syria

Syria ta kammala lalata dukkan makamai masu guba da ta mallaka tare da kayayyakin kera su kafin wa'adin da majalisar dinkin duniya ta deba ma ta.

Jami'an hukumar yaki da makamai masu guba (OPCW) sun ce bayan kwashe wata guda a kasar, sun amince an kammala lalata makaman kafin wa'adin daya ga Nuwamba ya cika.

An tura masu binciken makamai zuwa Syria ne bayan da aka zargi dakarun gwamnati da amfani da makamai masu guba akan fararen hula, abinda mahukunta suka musanta.

Rahotanni na cewa adadin makamai masu guba da Syria ta mallaka sun hada da ton 1,000 na iskar Sarin, da sulphur mustard da sauran dangin gubobi.