'Yan majalisar Turkey mata sun sa mayafi

Mayafi a majalisar Turkey
Image caption Mayafi a majalisar Turkey

Wasu 'yan majalisa mata hudu a Turkey sun halarci zaman majalisar da mayafai, a karo na farko tun 1999 lokacin da aka yi wa wata mai kishin Islama ihu a zauren.

Matan guda hudu, wadanda baki dayansu 'yan jam'iyyar Justice and Development Party ce ba su fuskanci wani bore ba.

Sauran 'yan majalisar sun kewaye su suna daukar hotuna.

A watan jiya ne Turkey ta dage haramcin sanya mayafi a wasu daga cikin gine-ginen hukuma amma har yanzu akwai masu jin zafin halatta wannan dabi'a ta Musulunci.