Dole Kenyatta ya gurfana a kotu --ICC

Shugaba Kenyatta a Kotu a Hague
Image caption Shugaba Kenyatta a Kotu a Hague

Kotun hukunta miyagun laifukka ta duniya, ICC ta janye wata shawara da ta zartar a baya, wadda ta amince wa shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya rika halartar wasu daga zaman shari'ar da ake masa.

Kotun a birnin Hague ta fitar da wata sanarwa tana mai cewa a yanzu ya kamata Mr Kenyatta , bisa ka'ida, ya kasance a kotun a duk lokacin da zata yi zama.

A watan jiya , alkalan kotun sun yanke hukuncin cewa ne zai iya halartar muhimmai daga zaman kotun ba duka ba.

Shi dai Mr Kenyatta ya kawo hanzarin cewa ne halartar zaman kotun zai shafi aikinsa na shugabancin kasa.

Ana zargin Mr Kenyatta ne da laifin ingiza mummunan tashin hankalin da ya biyo bayan zaben 2007.