JTF ta kashe 'yan bindiga biyu a Kano

Sojin Najeriya
Image caption Lokaci zuwa lokaci ana samun irin wannan fafatawa tsakanin sojin da ''yan bindiga

Rundunar tsaron hadin gwiwa JTF a Kano ta ce jami'anta sun kashe wasu 'yan bindiga biyu a wani sumame da jami'an suka kai wata maboyar yan bindigar a unguwar Gayawa.

Haka kuma rundunar ta ce ta kama wasu mutane biyu da take zargin suna shirin kai hari jihar Zamfara.

Tun da sanyin safiyar Talata ne dai mazauna unguwar ta Gayawa suka ce sun rika jin amon bindigogi da karar fashewar abubuwa a yankin nasu.

Rundunar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar.

A waje daya kuma hukumomin 'yan sanda a jihar Gombe da ke arewacin Najeriyar sun yi karin haske kan wani mummunan hari da wasu 'yan-bindiga suka kai jiya da dare a kauyen Bojude da ke karamar hukumar Kwami inda aka samu asarar rayukan mutane kimanin biyar da kuma dukiya.

'Yan-bindigar da suka yi dauki-ba-dadi da 'yan-sanda sun yi amfani da muggan makamai ciki har da abubuwa masu fashewa.