'Shinawatra zai koma Thailand daga gudun hijira'

Thaksin Shinawatra
Image caption Thaksin Shinawatra ya shafe shekaru biyar yana gudun hijira

Majalisar wakilan Thailand ta sanya hannu akan wani kudurin doka na yin afuwa, wanda idan ya samu mincewar majalisar dattawan kasar zai sharewa tsohon Firai mininstan kasar Thaksin Shinawatra hanyar dawowa gida daga gudun hijirar da ya yi na shekaru biyar.

Babbar jam'iyyar adawar kasar ta ' The Democrats' ta kauracewa zaman kuri'ar da aka kada a majalisar wakilan kasar, Inda jami'iyyar Mr Thaksin wacce a yanzu 'yar uwar sa Yingluck ke jagoranta take da rinjaye.

Wakilin BBC a Bangkok ya ce zai yi wahala a yi wa kudurin dokar wani kallo face wani yunkuri na dawo da Mr Thaksin gida,mutumin da jama'a da dama suke da ra'ayi irin na sa a Thailand a shekaru goman da suka gabata.

Karin bayani