Jamus na kokarin tattaunawa da Snowden

Image caption Edward Snowden

Ministan harkokin cikin gidan Jamus ya ce yana son shirya wata tattaunawa da tsohon jami'in leken asirin Amurka dake guje ma kamu, Edward Snowden, game da zargin da ake yi cewa Amurka ta rika satar sauraren magangun waya na shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel.

Hans-Peter Friedrich, ya ce duk wani bayani da hukumomin Jamus za su samu daga Mr Snowden, zai yi musu amfani.

Lauyan Mr Snowden dai ya ce ba zai iya zuwa Jamus ba daga Moscow, inda aka ba shi mafaka, amma a shirye yake ya bada nasa bahasin daga can.

'Magance matsalar'

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, ya yi alkawarin yin aiki tare da shugaba Obama domin kawo karshen abun da ya kira matakan da ba su dace ba da hukumar leken asirin kasar ke dauka.

A wani jawabi ta bidiyo da ya yiwa wani taron kasa da kasa a nan London, Mr Kerry ya ce a wasu lokutan aikin leken asirin da Amurka ke yi, yana wuce gona da iri.

Mr Kerry ne jami'in gwamnatin Amurka mafi girma mukami da ya yi magana kai tsaye a kan zarge-zargen da aka yi cewa Hukumar leken asirin Amurkar ta saurari maganganun waya na shugabannin gwamantocin kasashen dake kawance da ita.

Karin bayani