Zamu dauki matakai kan leken asiri - Kerry

Image caption John Kerry

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, ya yi alkawarin yin aiki tare da shugaba Obama domin kawo karshen abun da ya kira matakan da ba su dace ba da hukumar leken asirin kasar ke dauka.

A wani jawabi ta bidiyo da ya yiwa wani taron kasa da kasa a London, Mr Kerry ya ce a wasu lokutan aikin leken asirin da Amurka ke yi, yana wuce gona da iri.

Ya ce "Na yarda, kamar yadda shugaban kasa da kansa ya fadi, cewa a wasu lokutan abun yana wuce makadi da rawa; kuma za mu dauki matakan da suka dace domin hana sake aukuwar hakan".

Mr Kerry ne jami'in gwamnatin Amurka mafi girman mukami da ya yi magana kai tsaye a kan zarge-zargen da aka yi cewa hukumar leken asirin Amurkar ta saurari maganganun waya na shugabannin gwamnatocin kasashen dake kawance da ita.

Sai dai Mr Kerry din ya ce akwai bukatar a kara sa ido, saboda hakan na yin rigakafin hare-haren ta'addanci.

Karin bayani