An mikawa 'yan kasuwa harkar lantarkin Nigeria

Image caption An sha yunkurin inganta lantarki amma ba a yi nasara ba

A yau ne hukumar samarwa da rarraba wutar lantarki ta Nigeria PHCN ta mika kamfanonin da ke karkashinta ga masu zuba jari da suka sayi kamfanin daga gwamnati.

Sayar da hukumar dai wani mataki ne na inganta samar da lantarki ga al'umar kasar.

Kamfanin Sahelian Power SPV limited dai shi ne ya sayi kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano da ya hadar da jihohin Kano da Katsina da Jigawa, yankin da ke koma baya sosai a kasar wajen samun wutar lantaki.

A lokuta da dama gwamnatotin kasar daban-daban sun rika zuba makudan kudade a harkar samar da lantarkin domin inganta ta amma kwalliya ba ta biyan kudin sabulu ba.

Karin bayani