Nijar na makokin kwanaki uku

Gawarwaki a Nijar
Image caption An binne gawarwakin a Sahara

Gwamnatin Nijar ta bayyana makokin kwanaki uku domin jimamin mutane 92 da kishirwa ta hallaka a Sahara bayanda motocinsu su ka lalace.

Wata yarinya a cikin ayarin mai suna Shafa ta bayyana irin wahalar da ta su ka sha a tafiyar da mafi yawansu mata da kananan yara ne.

Shafa mai shekaru 14, ta ce motarsu ta lalace a kan hanyarsu ta zuwa Algeria kuma mahaifiyarta da kannenta mata biyu na daga cikin wadanda suka rasu, kuma da kanta ta birne su a cikin hamada.

Tace su da suka tsira sun shafe kwanaki biyu suna tafiya cikin hamada mai tsananin zafi, kuma babu mota ko daya da ta tsaya don taimaka musu.

Wani mai aikin ceto ya bayyana yadda suka yi ta ganin gawarwaki a cikin hamada sakamakon mummunan lamarin.