An kashe shugaban Taliban na Pakistan

Image caption Hakimullah Mehsud

Jiga-jigan kungiyar Taliban sun shaida wa BBC cewar an kashe Shugaban kungiyar na Pakistan, Hakimullah Mehsud a arewacin Waziristan.

Ya rasu ne sakamakon harin da Amurka ta kai wa gidansa da jirgi mara matuki.

Rahotanni sun ce an kashe mutane biyar a harin, ciki had da kanin Mehsud.

Dama dai Mehsud na cikin jerin hukumar tsaron Amurka FBI na 'yan ta'addan da ake nema ruwa a jallo inda a ka yi shelar ba da tukwicin dala miliyan biyar ga duk wanda ya taimaka a ka kama shi.

An kashe shi ne a ranar da gwamnatin Pakistan ta sanar da cewar ta tura wata tawaga don soma tattaunawar sulhu da 'yan Taliban.

Karin bayani