Roma ta kafa tarihi a gasar Serie A

Gervinho
Image caption Gervinho

Roma ta zamo kungiyar kwallon kafa ta farko a tarihin Serie A da ta yi nasarar lashe wasanni goman farko a jere, bayanda ta doke Chievo 1-0 ranar Alhamis.

Kwallon Marco Borriello ta farko a bana ita ce ta bai wa kungiyar da jagorantar rukunin Serie nasara kan kungiyar da ke can kasan tebur.

Roma, wacce ta jefa kwallaye 24 a ragar abokan karawarta sannan aka sa mat kwallo daya tak, ta yi wa Napoli da ke bin ta zarra da maki biyar.

Borriello ya ce "wannan tarihin da muka kafa abin alfahari ne sai dai yanzu abinda mu ka sa gaba shi ne mun samu nasarar shiga gasar zakarun Turai."