An sassauta dokar hana fita a Yobe

Harin Yobe
Image caption Harin Yobe

Rundunar Sojoji masu aikin tabbatar da tsaro ta musamman a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Nigeria, ta ba da sanarwar takaita dokar hana zirga zirga.

A yanzu rundunar ta ce jama'a zasu iya yin walwala daga Karfe shida na safe zuwa karfe shida na yamma.

Sannan dokar hana fitar za kuma ta soma aiki daga shida na yamma zuwa shida na safe.

A makon jiya ne dai rundunar ta sanya dokar hana zirga-zirga ba dare ba rana a garin Damaturu bayan wasu munanan hare-hare da 'yan bindigar da ake zargin mayakan Jama'atu Ahlis Sunnah lid Da'awati wal Jihad da ake wa lakabi da Boko Haram ne suka kai.

Daga bisani kuma rundunar ta sassauta dokar ta koma daga karfe hudu na yamma zuwa bakwai na safe.