Ana zaben kananan hukumomi a Enugu

Tashar zabe a Najeriya
Image caption Za a rufe runfunan zaben da karfe uku,sai dai kila a kara lokaci saboda jinkirin da a ka samu a wasu wuraren

A Najeriya, ana can ana gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar Enugu da ke kudu maso gabashin kasar.

Inda 'yan takara ke fafatawa domin dare kujerun shugabannin kananan hukumomi 17 da na kansiloli 260.

Rahotanni sun nuna cewa komi na tafiya lafiya, ko da yake an yi jinkirin fara zaben a wasu wurare.

Tun farko dai wasu jam'iyyun adawa sun yi korafin cewa an hana 'yan takararsu tsayawa ba bisa ka'ida ba.