Za a hada karfi don kawo karshen rikicin Iraqi

Hari a Iraqi
Image caption Iraqi da Amurka za su hada hannu wajen kawo karshen rikici a Iraqin.

Prime Ministan Iraqi Nouri al-Maliki da Shugaba Obama na Amurka sun gana a Fadar gwamnatin Amurkar dake white House.

Shugaba Obama ya ce sun tattauna ne a kan yadda za su yi aiki tare don kawo karshen tashe-tashen hankulan dake karuwa a Iraqi wanda dukkan Shugabannin biyu suka ce laifin kungiyar al-Qaeda ne.

Har ila yau kuma Shugaban na Amurka ya ce yana son Iraqi ta zartas da dokar zabe ta yadda 'yan kasar ta Iraqi za su tattauna bambance-bambancensu a siyasance a maimakon tashin hankali.

Prime Minista Malikin dai ya ce gwamnatinsa ta kuduri aniyar gudanar da zabuka da aka shirya a badi a cikin lokaci:

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba