An kama 'yan ci-rani a Nijar

jami'an Nijar a hamadar Sahara
Image caption 'Yan ci-ranin da a ka kama suna hannun 'yan sanda

Hukumomi a Niger sun kama yan ci-rani fiye da dari daya wadanda ke kan hanyarsu ta zuwa Algeria.

Hakan dai ya biyo bayan mutuwar mutane fiye da 90 da suka hada da mata da yara da suka rasu sakamakon Kishin ruwa.

Yayin da suke kokarin ketarawa ta hamadar Sahara wadanda aka gano bayan sun yi kwanaki da mutuwa.

Gwamnatin ta Niger ta kuma ce za ta rufe dukkan haramtattun sansanonin yan ci-rani da ke arewacin kasar da kuma hukunta wadanda ke safarar mutanen.

Karin bayani