Nijer za ta rufe sansanonin ci rani

Image caption Masu ci rani a Nijer na ketarewa zuwa wasu kasashe ta Sahara

Gwamnatin Nijer ta sanar da cewa za ta rufe dukkan sansanonin 'yan ci-rani dake arewacin kasar.

A wata sanarwa da aka karanta a talabijin na kasar, gwamnatin har ila yau ta sanar da cewa za a zakulo wadanda ke da hannu a kwasar 'yan ci-rani daga arewacin Nijer zuwa Algeria ko Libya a yi musu hukunci mai tsanani.

Gwamnatin ta ba da sanarwar ne kwanaki kalilan bayan an gano gawarwakin mutane 92 wadanda aka yi imanin cewa 'yan ci-rani ne a hamadar Sahara.

Ministan harkokin wajen kasar ta Nijer Mohammed Bazoum ya shaidawa BBC cewar a yanzu haka a garin Agadez kadai akwai 'yan ci-rani kimanin dubu biyar daga kasashe dabam-dabam na Afrika dake a wasu haramtattun sansanoni na 'yan gudun hijira.

Ministan harkokin kasashen waje na Jamhuriyyar Nijar, Mohamed Bazoum ya shaidawa BBC cewa kusan yan ci rani yan kasar Afrika dubu biyar ne suka yi carko carko a haramtattun sansanoni dake arewacin birnin Agadez kadai.

Karin bayani