An kashe jami'in Amurka a Los Angeles

Image caption An yi harbe harbe a filin jirgin saman Los Angeles

Hukumar sufuri ta jami'an tsaron Amurka ta fada a wata sanarwa cewa an kashe daya daga cikin jami'anta, an kuma raunata wasu da dama a harbe-harben da aka yi a filin jiragen sama na Los Angeles.

'yan sanda sun fada tun farko cewar wani ne dake dauke da bindiga shi kadai ya kai harin, lamarin da ya tsayar da tashin jiragen sama da dama a sassa dabam-dabam na Amurkar.

Jami'an 'yan sandan sun ce mutumin da ake zargi sunansa Paul Ciancia wani dan shekaru 23 da haihuwa.

Shugaban 'yan sanda dake filin jiragen saman na Los Angeles Patrick Gannon ya ce Paul Ciancia ya zaro wata karamar bindiga ya buda ma kansa hanya a wani wurin bincike na tsaro dake filin jiragen saman.

Karin bayani