Ana gab da kisan kiyashi a Afrika ta Tsakiya

'yan tawayen kungiyar Seleka
Image caption Jami'an Majalisar Dinkin Duniya sun ce, ''muddin ba a dauki mataki ba da wuri lamarin zai kazanta''

Manyan jami'an Majalisar Dinkin Duniya sun yi kashedi ga kwamitin sulhu na Majalisar cewar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya na neman afkawa wani mummunan rikici na addini.

Mai ba da shawara na musamman ga Majalisar Dinkin Duniyar a kan yadda za a kare afkuwar kisan kare dangi Adama Dieng ya ce al'ummomin Musulmi da Kirista na neman kashe junansu.

Ya ce, muddin kasashen duniya ba su tsoma baki ba, za a yi kisan kare dangi a kasar.

Kungiyar Tarayyar Afrika ta yi niyyar tura dakarun kiyaye zaman lafiya kimanin dubu ukku da dari shidda zuwa Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya wadda ta afka cikin wani yamutsi tun lokacin da 'yan tawaye suka hambarad da Shugaba Francois Bozize.