Amurka na so a dawo da dimokaradiyya a Masar

Image caption Kerry na yin ziyarar ne daidai lokacin da Morsi ke shirin gurfana a gaban kuliya.

Sakataren harkokin wajen Amurka,John Kerry, ya isa birnin Alkahira na Masar inda zai yi kira ga gwamnatin da soji ke marawa baya da ta dawo da mulkin dimokaradiyya a kasar.

Kerry dai shi ne babban jami'in gwamnatin Amurka da ke kai ziyara kasar tun da aka tumbuke gwamnatin zababben shugaban kasar, Mohamed Morsi, a watan Yuli, lamarin da ya sanya Amurka ta dakatar da tallafin miliyoyin dala da take bai wa kasar.

Ziyarar da Mista Kerry ke yi a Masar ta zo ne kwana guda kafin Mohammed Morsi ya gurfana a gaban kuliya bisa zargin tunzura mutane, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwa jama'a da dama a wajen fadar shugaban kasar a watana Disambar shekarar 2012.

Karin bayani