Ana hasashen husufin rana a yau

Husufin rana
Image caption Husufin rana a yau zai shafi sassa da da dabam dabam na duniya

Idan an jima da rana ne a yau Lahadi ake hasashen ganin Husufin rana a wasu sassan duniya da dama.

Masana ilimin halittun sararin samaniya sun ce lamarin zai shafi nahiyoyi da dama na duniya ciki har da Africa inda ranar gaba daya za ta buya.

Sai dai kuma sabanin yadda wasu mutane ke nuna fargabar ta afkuwar wasu hukunce-hukuncen Allah a lokacin husufin, masana kimiyyar sun bayyana cewar babu abinda zai faru.

A ranar 30 ga watan Maris ne na shekara ta 2006, aka samu husufin na rana a wasu sassan duniya ciki har da Nijeriya.