An kashe mutane fiye da 20 a jahar Borno

Image caption Harin da aka kai a Benisheik a watan Satumbar bana

'Yan bindiga da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne a kan babura wasu kuma a cikin akorikura sun diramma garin Bama dake jihar Borno inda suka kashe akalla mutane 23 suka kuma kona gidaje fiye da 100.

Rahotanni sun ce a makon daya gabata ne 'yan Boko Haram din kusan su 70 suka kaddamar da hari a Gulumba dake karamar hukumar Bama inda suka kashe mutane, tare raunata wasu sannan suka lalata dukiyoyin jama'a.

Wani mazaunin Bama ya shaidawa BBC cewar a ranar Alhamis da safe lamarin ya faru, inda mutanen da suka tsira da ransu suka nemi mafaka a kauyen Ali Chingori.

Sakamakon rashin layukan salula a jihar Borno dai, ba a iya samun bayanai a kan hare-hare a kan lokaci har sai bayan kwanakin da afkuwar lamarin.

Wannan harin na zuwa ne bayan da wasu 'yan bindiga da ake zaton 'yan Kungiyar Boko Haram ne suka farma tawagar 'yan biki wanda suka kashe mutane fiye da talatin.

Daga cikin wadanda suka rasu har da angon inda suke kan hanyar Bama-Banki suke komawa Jihar Borno.

Karin bayani