Ana binciken kisan Faransawa a Mali

'Yan jaridar Faransa da ka kashe a Kidal
Image caption 'Yan jaridar Faransa da ka kashe a Kidal

Rahotanni daga arewacin Mali na cewa ana binciken wadansu da ake zargi na da alaka da kisan 'yan jaridar Faransa guda biyu.

An dai samu gawar Ghislaine Dupont da Claude Verlon ne kusa da garin Kidal a ranar Asabar, bayanda wasu 'yan bindiga suka cafke su.

Sun je Kidal ne domin tattaunawa da wani kakakin kungiyar 'yan aware ta abzinawa (MNLA).

Ministan harkokin kasashen waje na Faransa Laurent Fabius ya ce an kama wadansu mutane kuma ana yi musu tambayoyi.