Isra'ila ta bayar da kwangilar gina matsugunai

Image caption Palsdinawa na adawa da kwangilar gina matsugunan Yahudawa

Isra'ila ta bayar da kwangilar gina wasu matsugunan yahudawa fiye da dubu daya da dari bakwai a yankin da ta mamaye na Gabar yammacin Kogin Jordan da gabashin birnin Kudus.

Shawarar cigaba da gine-ginen wadda Amurka ta nuna adawa da ita ta zo ne gab da ziyarar da Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry zai kai a yankin.

Hukumar mulkin Palasdinawa ta yi barazanar gabatar da batun gaban Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.

To amma Pirai Ministan Isra'ila Binyamin Netanyahu ya ce shi dama bai taba alkawarin dakatar da gine-ginen ba a lokacin tattaunawar sulhu da Palasdinawa.

Karin bayani