Ana tuhumar mutane hudu kan harin Westgate

Rukunin kantunan Westgate
Image caption Rukunin kantunan Westgate

An tuhumi mutane hudu bisa zargin kai hari a rukunin kantunan Westgate da ke Nairobi, babban birnin Kenya inda fiye da mutane 60 suka mutu.

Ana zargin 'yan kasashen wajen hudu ne da laifin taimakawa kungiyoyin 'yan ta'adda a Kenya tare da shiga kasar ba da izini ba.

Mutanen da suka hada da Mohammed Ahmed Abdi, Liban Abdullah, Adnan Ibrahim da Hussein Hassan 'yan kabilar Somali ne amma dai ba'a baiyana kasashensu ba.

Gaba daya su hudun sun musanta tuhumar da ake yi musu.

Sai dai babu wani daga cikinsu da ake zargin yana cikin 'yan bindigar da suka kai farmaki a rukunin kantunan.