John Kerry yana ziyara a Saudiyya

Kerry da Sarki Abdullah
Image caption Sakataren harkokin wajen Amurka yana ziyara a Saudiyya

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya isa kasar Saudiyya domin farfado da dadaddiyar alakar da ke tsakani kasashen biyu bayan da aka fara samun tangarda a baya bayan nan.

Batun kasashen Syria da Iran na cikin muhimman abubuwan da zai tattauna da Sarki Abdallah.

A cikin watan da ya gabata, kasar Saudiyyar ta ki amincewa da kujerar da aka ba ta a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya bayan Amurka ta yanke shawarar kin kai hare-hare ta sama a kan sojojin Syria.

Wakilin BBC a ma'aikatar harkokin wajen Amurka ya ce Saudiyyar kuma ta damu da kyautatuwar dangantakar da aka samu baya-bayan nan tsakanin Amurkar da Iran tun bayan hawan Shugaba Hassan Rouhani kan karagar mulki.

Karin bayani