Gobara ta tashi a babban bene a Lagos

Image caption 'Yan kwana-kwana na kokarin kashe gobarar

Gobara ta tashi a wani babban bene mai hawa 15 dake unguwar Marina a jihar Lagos dake kudancin Najeriya.

Gobarar wacce ta soma daga hawa na biyu a safiyar litinin, ta ci gaba da yin barna kafin 'yan kwana-kwana su isa wajen don kokarin kashe ta.

Benen da ake kira 'Great Nigeria House' na daga cikin tsofaffin gine-ginen da suke Lagos, cibiyar kasuwancin Nigeria.

Kawo yanzu dai babu rahoton hasarar rayuka sakamakon gobarar.

A cikin ginin, akwai manyan ofisoshi na bankuna da kamfanonin 'yan kasashen waje musamman 'yan China.

Karin bayani