Morsi: An dage shari'arsa har sai 2014

Magoya bayan Muhammad Morsi
Image caption Morsi zai shiga kotu

An dage shariar hambararren shugaban kasar Masar dan kishin Islama Muhammad Morsi, da ake zargi da ingiza kisan masu zanga-zanga.

Kafafen yada labarai na gwamnati sun rawaito cewa an dage shariar ne zuwa takwas ga Janairun 2014 domin bai wa lauyoyi damar nazari kan tuhumar.

A zaman kotun, Mr. Morsi ya ki sanya kayan da ake baiwa wadanda ake tuhuma kuma ya shaidawa kotu cewa har yanzu shi ne halattacen shugaban kasar Masar.

An gurfanar da Mr. Morsi ne tare da wasu jagororin kungiyar 'yan uwa Musulmi su 14.

Rahotanni sun ce an cigaba da zanga-zangar goyon bayan Morsi a tsakiyar birnin Cairo bayan dage shari'ar.