An tsaurara tsaro a Masar saboda shariar Morsi

Matakan tsaro a Masar
Image caption An tsaurara matakan tsaro saboda shariar Mohammed Morsi a Masar

Jami'an tsaro a kasar Masar sun kara tamke damarar tsaro gabanin fara tuhumar hambararren Shugaban kasar dan kishin Islama Mohammed Morsi

An caje shi da wasu manyan jami'an kungiyar Muslim Brotherhood su 14 da laifin ingiza kisan masu zanga-zanga.

Magoya bayan Mr Morsi sun yi kiran da a gudanar da babbar zanga-zanga a kusa da wurin da za a gurfanar da shi a birnin Alkahira da kuma wasu sassan kasar.

Ba a dai tantance ba ko Mr Morsi din, zai bayyana a Kotun.

Ana tsare da shi a wani boyayyen wuri tun lokacinda sojoji suka hambarar da shi a cikin watan Yuli.

Karin bayani