Bakuwar cuta ta bulla a Nijar

Mara sa lafiya a Nijar
Image caption Mara sa lafiya a Nijar

Hukumomin kiwon lafiya a Nijar sun tabbatar da bullar wata sabuwar cuta a cikin jihar Tillabery da kawo yanzu likitoci ba su kai ga tantance ko wace iri ba ce.

Alamomin cutar sun hada da zazzabi da amai da kuma zubar jini ta hanci da baki.

Mutane bakwai daga cikin sama da ashirin da suka kamu, sun rasu.

Ma'aikatar lafiya ta Nijar da taimakon hukumar lafiya ta duniya, WHO na ci gaba da bincike.