Arangamar 'yan sanda da sabuwar PDP

Gwamnonin sabuwar PDP
Image caption Gwamnonin sabuwar PDP

'Yan sanda a Najeriya sun yi yunkurin hana wani taron gwamnoni bakwai na tsagin sabuwar PDP da suka bijirewa jam'iyyar PDP mai mulki.

A daren Litinin ne DPO na Asokoro ya jagoranci tawagar 'yan sanda zuwa masaukin gwamnan jihar Kano da ke Abuja domin hana taron, amma bai yi nasara ba.

DPO Nnana Ama ya ce an turo shi ne ya hana taron ko kuma ya kama gwamnonin saboda gidan ba ofishin jam'iyyar siyasa ba ne.

Mulkin kauyanci

A cewar daya daga cikin gwamnonin, Sule Lamido na Jigawa: "Muna ganin mulkin kauyanci" domin raini a ce DPO ya zo ya tashi taron gwamnoni.

Ya kara da cewa dama taron na tattaunawa ne game da zaman sulhu tsakaninsu da shugaban kasa Goodluck Jonathan game da makomarsu a siyasance.

Mai masaukin baki, gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya ce wannan yunkurin "rashin iya aiki ne domin wanda ka ke kokarin sulhu da shi bai kamata ya turo ma 'yan sanda ba."

Wannan dai shi ne karo na hudu cikin watanni biyu da bangaren na sabuwar PDP ke arangama da jami'an tsaro a Abuja.