Rikicin addini a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Dakarun Seleka
Image caption Dakarun Seleka

Ana fargabar barkewar rikicin addini a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya bayanda aka hambarar da shugaba Francois Bozize a watan Maris, kamar yadda wakilan BBC Laeila Adjovi da Abdourahmane Dia suka rawaito.

Bossangoa, mahaifar hambararren shugaban kasar, ta zama kango; gine-gine, tituna, da kasuwanni duk ba kowa.

Amma a tsakiyar Bossangoa, ana hada-hada a cocin Katolika.

Teloli, masu gyaran gashi, da masu sayar da abinci da sigari na gudanar da sana'o'i daf da dubunnan shudayen tantuna rufe da ledoji masu tambarin asusun yara na majalisar dinkin duniya, Unicef.

Fiye da Kiristoci dubu 35 ne ke fake a nan, bayanda 'yan tawayen Seleka, wanda suka hambarar da gwamnatin Mr. Bozize suka kai hari gidajensu.

Adadin na cigaba da karuwa domin ko a makon jiya mata da kananan yara kimanin 1,000 ne suka isa sansanin bisa kiyasin kungiyoyin cigaban al'umma.

Image caption Michel Djotodia na shan rantsuwa a matsayin shugaban kasa

Sai dai mazauna sansanin na fargabar barin cocin katolikan, koda kuwa gidajensu ba nisa.

'Shugaba Musulmi na farko'

Nina Saragba na sharbar kuka jikin bukkarta lokacinda take magana da BBC.

Ta ce yanzun nan ta samu labarin an harbe dan uwanta har lahira lokacinda ya yi kokarin shiga gari.

Sai dai Allah ya takaita, domin daga bisani an same shi da ran sa kodayake ya sha dukan tsiya.

Mazaunan sun ce irin wadannan hare-haren sun zama ruwan dare -da zarar sun bar cocin na Katolika, mayakan Seleka na iya tsare su, dukansu, ko kuma su harbe su, matukar dai aka danganta su da kungiyar 'yan banga ta Kirista mai suna anti-balaka.

Wannan na rura wutar daukar fansa a cikin sansanin.

"Ina son zama dan tawaye in kashe 'yan Seleka. Mun sha wuya sosai. Musulmi abokan gabarmu ne." in ji wani mutum mai shekaru 20.

Tun bayan samun 'yanci daga mulkin mallakar Faransa a 1960, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ke fama da juyin mulkin soji da kuma yakin basasa.

Sai dai wannan ne karo na farko da rikicin ya dauki sigar addini a kasar da ake wa take da zuciyar Afirka.

Kiristoci masu rinjaye da Musulmi mara sa rinjaye na zaman lafiya da juna har Maris 2013 lokacin da shugaban Seleka Michel Djotodia ya kwace mulki bayanda dakarunsa suka mamaye Bangui, babban birnin kasar.

Mr. Djotodia shi ne Musulmi na farko da ya mulki kasar, inda ya nada kansa a matsayin shugaban rikon kwarya tare da kafa gwamnatin da ya ce za ta gudanar da zabe.

Gwamnatin na musanta cewa ta na nuna bambanci ga wani addini, amma dai ta ce tabbas rikici tsakanin al'ummomi na karuwa.

Image caption Mayakan kungiyar Seleka

Tana kallon anti-balaka a matsayin wata sabuwar kungiyar 'yan tawaye, da magoya bayan Mr. Bozize suka kafa a mahaifarsa ta Bossangoa mai nisan kilomita 400 arewa da Bangui.

Mr Djotodia ya yi kokarin kwantar da hankalin kasashen duniya ta hanyar sanar da rushe rundunar Seleka.

Mahukunta sun ce an karbe makaman mafi yawan 'yan Seleka tare da zaunar da su a barikokin soji.

A Bossangoa kowanne bangare na cikin fargaba.

A lokacin sallar juma'a, mutane na barin takalmansu a waje amma ban da bindigoginsu.

'Rundunar AU'

Khadija al-Hadj Abdou, matar wani mai kiwon shanu, na cikin matukar damuwa lokacin da ta ke bamu labarinta sanye da mayafi launin ja da ruwan ganye.

Ta ce 'yan bangar anti-balaka sun kai farmaka kauyensu a farkon Satumba.

An harbe ta a wuya kuma nan take ta suma. Bayan farfadowarta ta tarar da gawarwakin babanta, mijinta, da 'ya'yanta a kewaye da ita.

Yanzu ita kadai ce ta raga cikin danginta.

An kuma kai irin wannan harin a birnin Bouca kimanin kilomita 250 daga Bangui.

Wani Musulmi, Mustapha Mohammed ya ce ya shaida kisan gillar mahaifinsa, wanda shi ne dagacin kauyensu ranar 9 ga Satumba.

Ya tsira ne sanadiyyar makwabtansa Kiristoci wadanda su ka sanar da Musulmi cewa ga 'yan bindiga nan za su kawo musu hari.

A wannan ranar ne kuma Musulmi suka kai harin fansa kan Kiristoci.

Image caption Hambararren Shugaban kasa, Francois Bozize

Aukin Nountabaye, wani malamin coci a Bouca, ya ce ya samu tserewa bayan da Musulmi suka afka ma sa.

Ya gudu daga Bouca, bayan kwanaki hudu ya isa Bangui - inda babu rikici tsakanin Kirista da Musulmi sai dai zaman takon saka.

Fiye da mutane 200 ne aka ce sun gudu zuwa Bangui bayanda rikici ya barke a Bouca.

Mr Mohammed da Mr Nountabaye jiga-jigan wata kungiyace da aka kafa a Bouca domin kyautata dangantaka tsakanin Kirista da Musulmi.

Sun ce akwai rashin yarda tsakanin al'umomin da suka zauna lafiya da junansu a baya.

Shugaban kungiyar, Gourna Zako Justin, ya bukaci gwamnatin rikon kwaryar da ta turo wata "rundunar 'yan ba ruwanmu" zuwa Bouca, abinda ke nuna sojoji su ma su na nuna bangaranci.

Karuwar rashin tsaro da kuma zargin gwamnati ba ta da iko kan dakarunta ya sa an matsawa kasashen duniya da su kai wa fararen hula dauki.

A makon jiya, Majalisar dinkin duniya ta amince da rundunar soji ta musamman mai dakaru 250 domin kare ma'aikatanta da ke jamhuriyar.

Kungiyar kasashen Afrika Au ta tura dakarun tabbatar da zaman lafiya 2,100 sai dai kawo yanzu ba ta cika alkawarin da ta yi na kara adadinsu zuwa 3,600 ba.

Image caption An girke a Bangui

Haka kuma jagororin yankin ba su bullo da wani shiri na kawo zaman lafiya a kasar ba.

Jamhuriyar Afrika ta Tsakiyar dai na makwabtaka da kasashe bakwai - Kamaru, Sudan ta kudu, Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo, Chad, Uganda da Congo-Brazzaville.

Da yawa daga cikin makwabtan na fama da tawayen da ya raba dubunnan daruruwan mutane da matsugunansu.

Don haka barkewar rikici a jamhuriyar zai rura wutar rikicin yankin.

A makon jiya, daraktan agaji na majalisar dinkin duniya John Ging ya baiyana lamarin da kasar ke ciki a matsayin "mai rudarwa."