Boko Haram ce ta kai harin Damaturu

Image caption A sabon Videon Boko Haram Shekau ne ya jagoranci harin Damaturu

Shugaban Jama'atu Ahlis sunna lid daawati wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram, Abubakar Shekau ya yi ikirarin cewa shi ya jagoranci harin da aka kai a Damaturu babban birnin Jihar Yobe a wani sakon Video da ya fitar a daren Litinin.

A faifan videon, Shugaban Kungiyar Boko Haram ya ce batun sulhu da mahukunta a Najeriya ke cewa ana yi ba gaskiya bane suna yin hakane inji shi don raba kan masu fafutukar.

Wannan sakon ya zo ne kwana daya bayan da wasu 'yan bindiga da ake zaton yan Kungiyar Boko Haram ne suka farma tawagar 'yan biki wanda suka kashe mutane fiye da talatin.

Daga cikin wadanda suka rasu har da angon inda suke kan hanyar Bama-Banki suke komawa Jihar Borno.

Sai dai Rundunar Sojin Najeriya na cewa mutane biyar ne suka rasu.

A wata sanarwa da kakakin Rundunar ya fitar Lt Col. Mohammed Dole, ya ce an gano gawarwakin kuma an mika su zuwa garin Bama.

Karin bayani