Jirgin leken asirin Amurka mai gudun tsiya

Lockheed Martin
Image caption Kamfanin Lockheed Martin mai kera jiragen yakin Amurka

Kamfanin Lockheed Martin ya fara aikin kera jirgin da zai gaji jirgin leken asiri samfurin Blackbird SR-71 mai gudun da ya zarta na sauti.

Sabon jirgin samfurin SR-72 wanda ba shi da matuki zai iya gudun kilomita 5,800 a cikin sa'a daya.

Kamar dai jirgin da zai maye gurbinsa, SR-72 zai rinka leken asiri ne daga koluluwar sama sai dai za'a iya makala masa makamai domin kai hari.

Lockheed ya ce nan da 2030 sabon jirgin zai fara aiki.

'Gudun tsiya'

Ana aikin kera SR-72 din ne a cibiyar bincike ta Skunk Works mallakar Lockheed Martin da ke California inda aka kera jirgin Blackbird na asali.

Jirgin ya fara tashi ne a 1964 kuma da shi rundunar sojin saman Amurka ta dogara wurin leken asiri har zuwa 1998. Ya kan yi nisan mita dubu 24 a sama tare da gudun kilomita 2,900 cikin sa'a daya.

Lockheed Martin ya ce SR-72 zai tashi koli kamar SR-71 amma zai nunka shi a gudu ta yadda zai iya tafiyar kilomita 5,500 daga New York zuwa London a kasa da sa'a daya, sabanin sa'o'i uku da jiragen fasinja kan yi.

Jiragen leken asiri na yanzu kan iya daukar hotunan kasashen abokan gaba sai dai tsawon lokacin da su kan dauka kan su koma gida na takaita amfanin hotunan da suka samo.

Sabanin haka, a cewar Lockheed Martin, SR-72 "na da matukar saurin da zai dawo da rahotanninsa kafin abokin gaba ya samu lokacin buya ko daukar wani mataki."