Kakakin majalisar dokokin Taraba ya rasu

Image caption Margayi Haruna Tsokwa

Shugaban Majalisar dokokin jihar Taraba, Haruna Tsokwa ya rasu sakamakon rashin lafiya.

Mr Tsokwa ya rasu a ranar Litinin da safe a babban asibitin gwamnatin tarayya dake Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

Rahotanni sun nuna cewar a ranar Alhamis din data gabata ne aka garzaya da Mr Tsokwa asibiti bayan da rashin lafiyarsa ta kara tsanani.

Margayi Haruna Tsokwa ya kasance mai goyon bayan mukaddashin gwamnan jihar Taraba, Garba Umar, tun lokacin da jihar ta fada cikin rikicin siyasa sakamakon rashin lafiyar gwamna Danbaba Suntai.

Karin bayani