Hukuncin kisa kan sojoji 150 a Bangladesh

Image caption Boren ya janyo hasarar rayuka da dama

Wata kotu a kasar Bangladesh ta yankewa sojoji fiye da 150 hukuncin kisa, saboda mummunan boren da suka yi har aka zubar da jini a shekara ta 2009.

Sannan kuma an yankewa wasu sojojin fiye da 150 wadanda galibinsu masu gadin kan iyaka ne hukuncin daurin rai-da rai.

Haka nan kuma ana tuhumar wasu fararen hula 23 da laifin hada baki da sojojin.

Tuni dai aka yankewa wasu sojojin 823 hukunci a wata kotun farar hula.

Boren da sojojin suka yi na tsawo sa'o'i 30 a kan albashi a Dhaka ya janyo mutuwar mutane 74 cikinsu 57 sojoji ne.

Karin bayani