Ban Ki Moon na ziyartar kasashen Sahel

Image caption Ban Ki Moon

Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon, ya fara wata ziyara a kasar Mali wadda za ta kai shi zuwa kasashe biyar na yankin Sahel.

Kasashen da Mr Ban zai ziyarta tare da shugaban bankin duniya da shugabannin hukumomin zartarwa na kungiyar tarayyar turai sun hada da Niger da Chadi da Burkina Faso.

Baya ga batun tsaro ana kuma sa ran shugabannin za su tattauna da hukumomin na Nijar a kan wani tsari na habaka tattalin arziki da kyautata jin dadin rayuwar jama'a ta hanyar inganta tsaro a yankin sahel.

Ministan harkokin wajen Niger, Malam Bazoum Mohammed a hirarsa da BBC ya ce ziyarar za ta taimakawa kasashen Sahel wajen samun tallafi daga Majalisar Dinkin Duniya.