'Ba mu tattauna da Shekau ba'

'Yan Kungiyar Boko Haram
Image caption Kwamitin bai samu damar ganawa da Shugabannin Kungiyar Boko Haram ba

Kwamitin da Shugaban Nigeria ya kafa domin tattaunawa da kungiyar Jama'atu Ahlis sunnah lidda'awati wal jihad da aka fi sani da Boko Haram da kuma gabatar da shawarwari akan yadda za'a tunkari kalubalen tsaro a arewacin Najeriya ya gabatar da rahotansa.

Shugaban kwamitin, ministan ayyuka na musamman Kabiru Tanimu ya ce kwamitin bai samu tattaunawa da shugabannin kungiyar ba duk da kokarin hakan da ya yi.

Sai dai a cewar Ministan wasu daga cikin fitattun 'yan kungiyar na tsare da na waje, sun amsa kiran da akai musu, kuma sun amince cewa tattaunawa ita ce mafita ta warware tashe tashen hankulan da ake fuskanta

Kwamitin ya kuma baiwa shugaban kasar shawarar kafa wani kwamitin mashawarta, wanda zai dora daga inda suka tsaya.

'Diyya'

Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya ce zasu yi nazarin rahotan kwamitin kuma ya ce ya amince da shawarar da kwamitin ya bayar na kafa kwamitin mashawarta na dindindin da zai ci gaba da gudanar da wannan aiki.

Sai dai shugaban kasar ya ce gwamnati ba zata biya wadanda rikicin ya shafa diyya ba sai dai ta ba su tallafi.

A watan Afrilun daya gabata ne shugaban Najeriya ya kafa kwamitin da ya dorawa alhakin tattaunawa da Kungiyar da kuma lalubo hanyoyin da za'a magance halin da ake ciki na tabarbarewar tsaron a arewacin Najeriya.

Kwamitin dai ya sha suka daga bangarori da dama a cikin kasar, inda wasu su ka yi zargin ba zai tabuka komai ba.

Kazalika Shugaban Kungiyar ta Jama'atu Ahlis sunna lidda'awati wal jihad Imam Abubakar Shekau a lokuta da dama ya sha fitowa a faifan bidiyo yana musanta cewar ana sulhu da su.

Karin bayani