Congo:'Yan M23 sun kwance damara

Yara na wasa kan tankar yakin 'yan tawayen M23 da aka kona
Image caption Yara na wasa kan tankar yakin 'yan tawayen M23 da aka kona

Kungiyar 'yan tawayen M23 ta Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo ta ce ta kawo karshen tayar da kayar baya, sa'o'i kadan bayan da gwamnatin kasar ta ce ta murkushe kungiyar da karfin soji.

A wata sanarwa, kungiyar ta ce yanzu za ta dauki "matakan siyasa zalla" domin cimma bukatunta, kuma ta umarci mayakanta da su ajiye makamai su koma gidajensu.

Gwamnatin ta ce tsirarun 'yan tawayen da suka ja daga a gabashin kasar sun mika wuya wasu kuma sun tsere sun ketare iyaka cikin dare.