Najeriya za ta ci gaba da hulda da ICC

Kotun laifukan yaki dake Hague
Image caption Kasashen Afirka su na zargin ICC da bi- ta- da- kulli

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa kasar ba ta da niyyar fita daga sahun kasashe masu martaba Kotun hukunta laifukan yaki ta duniya da ke Hague.

Najeriyar ta ce tana goyon bayan manufofin kotun don haka za ta ci gaba da mu'amala da ita.

Shugaban Najeriya Dr Goodluck Jonathan ne ya jaddada dukufar kasar wajen ci gaba da hulda da Kotun hukunta laifukan yaki ta Kasa da Kasa dake Hague lokacin da Shugaban Kotun Mr. Sang Hyun Song ya kai masa ziyara a fadarsa.

Shugaban ya ce Najeriya za ta dinga goya wa kotun baya tare da kare manufofinta.

Kasashen nahiyar Afirka da dama ne ke zargin kotun na yiwa shugabannin kasashen Afirka bi -ta- da- kulli.

Karin bayani