An gaza tsayar da ranar taro kan Syria

Lakhdar Brahimi
Image caption Lakhdar Brahimi

Bayan da aka kashe yini guda ana tattaunawar diplomasiyya ka'in-da-na'in, an gaza tsayar da ranar ada aka dace ana jira ta fara shawarwarin sulhu kan Syria.

Bayan tataunaunawar a Geneva da ta hada jami'ai daga kasashen Amurka da Rasha da sauran kasashen masu wakilci a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, wakilin kasashen duniya kan rikicin Syriar, Lakhdar Brahimi ya ce yayi fatan ya bada sanarwar ranar da aka tsayar a yau, amma hakan bai yiwu ba.

Sai dai ya ce yana fatan kafin nan da karshen wannan shekara za a gudanar da wannan taro.

Daga cikin abubuwan dake tarnaki ga taron akwai rarabuwar kawuna tsakanin 'yan adawa, da kuma jan kafar da Syria ke yi kan batun kafa gwamnatin rikon kwarya.

Karin bayani