'Yan Syria na matukar bukatar agaji

Yan kasar Syria na cikin kuncin rayuwa
Image caption Yan kasar Syria na cikin kuncin rayuwa

Babbar jami'ar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ayyukan agaji Valerie Amos, ta gayawa kwamitin sulhu na Majalisar cewa sama da mutane miliyan tara watau kimanin kashi 40 na mutanen Syria a yanzu na bukatar agaji.

Fiye da rabin adadin nan, mutane ne da yaki ya daidaita wadanda ke zaune a cikin kasar ta Syria.

Valerie Amos, ta ce yanayin ya yi saurarin tabarbarewa, ta kuma yi kira ga kwamitin sulhun ya matsa lamba a kan 'yan kasar ta Syria su kyale hukumomin agaji su shiga yankunan da aka mamaye ba tare da wata tsangwama ba.

Haka kuma ta yi kira da a dakatar da fadan, don bayar da damar kwashe fararen hula da kuma kai kayan agaji.

Karin bayani