Sarakunan Gargajiya na taro a Sokoto

Image caption Sarkin Musulmi, Sultan Saad Abubakar III

Sarakunan Gargajiya daga ko'ina a Nigeria sun soma taro a birnin Sokoto dake arewacin kasar don tattauna kalubalen da kasar ke fuskanta.

Taron na zuwa ne a daidai lokacin da sassa daban-daban na kasar ke fama da matsalolin tsaro, inda masu sharhi ke cewar Sarakunan nada rawar da zasu taka wajen magance matsalar.

Sarakunan wadanda suke neman a shata masu wani matsayi a cikin tsarin mulki na taron ne domin tattauna kalubalen da kasar ke fuskanta.

A kan dai zargi sarakunan da rashin wani abun azo a gani don shawo kan matsalolin kasar ke fama tashi da su a baya bayan nan.

Karin bayani