An tsare wanda ya kashe dan Nigeria a India

Image caption Pirai ministan India, Manmohan Singh

'Yan sanda a jihar Goa ta India sun tsare mutumin da su ke zargin yana da hannu wajen kashe wani dan Najeriya a makon da ya gabata, lamarin da ya janyo 'yan Najeriya su kayi zanga-zanga a yankin.

Sakamakon afkuwar lamarin, 'yan sanda sun tsare 'yan Najeriya da dama wadanda suka yi boren tare da rufe wata babbar hanya na tsawon sa'o'i.

Jakadan Najeriya a India ya ce yana fargaba a kan tsaron 'yan Najeriya a Goa, inda ya bayyana tsare 'yan kasar a matsayin abinda ya kara rura wutan rikicin.

Wani minista a jihar Goa tunda farko ya bayyana 'yan Najeriya dubu 40 dake zaune a India a matsayin 'cutar daji'.

'Yan sanda sun ce kisan na da nasaba da dilolin miyagun kwayoyi dake hamayya da juna.

Karin bayani